
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yi watsi da tuhume-tuhume guda takwas da aka gabatar akan wanda aka yi zargin Darakta-Janar ne na hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi, wadda Gwamnatin Tarayya ta shigar.
Alƙalin ya ɗauki wannan mataki ne bayan gwamnatin ta gabatar da wata buƙata da kuma sharaɗin za a mayar da wanda ake zargin zuwa Babbar Kotun Abuja domin fara sabuwar gurfanarwa.
A yayin zaman na ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, Lauya mai kare ɓangaren gwamnati tarayyar, Rotimi Oyedepo (SAN), ya gabatar da ƙorafin neman a kawo ƙarshen tuhume-tuhumen a kotun. Ya shaida wa alƙalin cewa Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, ya yi nazari akan takardar ƙarar Adeyemi da wanda Sufeto Janar na Ƙasa ya shigar, inda aka gano waɗansu kurakurai.
Daga dalilan, akwai zargin takardun da Adeyemi ya yi aiki da su a matsayin na bogi wajen gudanar da harkokinsa, wanda Babbar Kotun Abuja ce ya dace a kai wa ƙara a madadin Babbar Kotun Tarayya.
Daraktan Shari’o’in Al’umma na Tarayya (DPPF), ya ce an shigar da sabuwar ƙara a Babbar Kotun ta FCT kuma za a gurfanar da Adeyemi a matsayin fara sabuwar shari’a. Akan haka ne ya buƙaci alƙalin kotun tarayyar da ya yi watsi da shari’ar kamar yadda doka ta buƙata. Ganin cewa babu wani inkari daga Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, Mai Shari’a Umar ya kori ƙarar bisa tsarin kotu.
