Daga USMAN KAROFI
Wata kotun tarayya da ke Ribas ta yi watsi da ƙarar da wasu ‘yan majalisa masu biyayya ga Gwamna Siminalayi Fubara suka shigar, inda suke ƙalubalantar matsayin ‘yan majalisar 27 da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Emmanuel Obile, ya bayyana cewa ‘yan majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar, Martins Amaewhule, har yanzu sahihan mambobin majalisar ne, yana mai cewa babu wani tanadi na kundin tsarin mulki da suka karya wanda zai tilasta musu barin muƙamansu.
Hukuncin na biyo bayan matsayar Kotun Ƙoli a watan Fabrairu, wadda ta gaza karɓar buƙatar Gwamna Fubara na tsige waɗanda suka sauya sheka. Wannan hukunci na yanzu ya ƙara tabbatar da matsayin ‘yan majalisar ɓangaren Wike, duk da ci gaba da taƙaddama tsakaninsu da ɓangaren gwamna Fubara.
