Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin tarayya za ta gina tagwayen hanya daga Zaria zuwa Malumfashi da kuma gidan Mutum Ɗaya zuwa Funtua.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da haka bayan ya ƙaddamar da hanyar ratse mai tsawon kilomita 24 da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta gina a Katsina.
Haka kuma ya bayyana cewa hanyar Katsina zuwa Kano da hanyar Ƙankara zuwa Katsina za a cigaba da aikin.
Sai Tinubu ya yabawa gwamnan kan nasarorin da ya samu wajen aiwatar da ayyukan da suka taɓa rayuwar al’ummar Jihar Katsina.
Ya bayyana Dikko Raɗɗa a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana da kowa zai yi alfahari da shi.
Tinubu ya ce wannan hanya da cibiyar kayan Noma za su bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Shugaban ƙasan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin tarayya za ta taimakawa gwamnatin jihar wajen kawo cigaba ta kowane fanni a jihar.
Haka kuma ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na iyaka ƙoƙarin ta wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar,ya yabawa gwamnan bisa matakan da ya ɗauka kan harkar tsaro a jihar.
A nasa jawabin gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da cewa da hawan su gwamnati zuwa yanzu ya gina hanyoyi mai tsawon kilomita 160 a faɗin jihar.
Sun kuwa haɗa da tagwayen hanyoyi da hanyar ratse a sassan jihar.
