Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna jin daɗin sa gami da farin ciki a lokacin liyafar cin abinci da gwamnatin Jihar Katsina ta shirya ma sa.
“An nishaɗantar da mu na yi farin ciki da hakan na ji kamar ina gida saboda Katsina tamkar gida ne a waje na”. In ji shugaban ƙasar.
Kawo yanzu shugaba Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Katsina ta aiwatar, shugaban ya kuma gana da masu ruwa da tsaki a jihar don lalubo hanyar daƙile hare haren ‘yan bindinga da ya addabi al’ummar jihar.
A nan gaba kaɗan, ana sa ran shugaba Tinubu zai halarci ɗaurin auren ‘yar gwamnan jihar ta Katsina kafin ya koma Abuja.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana cewa kalaman Tinubu bai rasa nasaba da nishaɗantawar da fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya yi a wurin taron.
Blueprint Manhaja ta ga wata sabuwar waƙar Rarara inda mawaƙin ya waƙen shugaban ƙasar cikin harshen Yarabanci, an ga gwamnan Juhar Katsina Dikko Umar Raɗɗa tare da wasu gwamnoni da suka halarci taron na murmushi, su na tafa hannayensu a yayin da aka ga shugaban ƙasar na murmushi tare da yin tafi tamkar ya tashi ya ɗan rausaya a lokacin da mawaƙin ke rera waƙar mai suna ‘Omo ologo’ wadda yanzu haka ta karaɗe shafukan soshiyal midiya.
