Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A ƙarshen makon da ya gabata, na samu damar halartar babban taron baje-kolin fasahohin marubuta da masu ƙirƙira daga mawaƙa da manazarta, da suka hallara a birnin Zazzau da ke Jihar Kaduna, wanda aka yi wa laƙabi da ZABAFEST. A yayin taron, an gudanar da abubuwa da dama da suka haɗa da tattaunawa tsakanin marubuta da manazarta game da gudunmawar marubuta littattafan Hausa ga cigaban al’adun al’ummar Arewa. Fitaccen malamin jami’ar nan mai nazarin adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Muhammad Malumfashi da Sarkin Mawallafan Arewa, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) da Safiyya Jibrin Abubakar su ne suka tattauna game da tasiri da ƙalubalen harkar rubutun adabi a jiya da yau.
Wani muhimmin batu da ya taso a ƙarshen tattaunawar shi ne batun muhawarar da ake tattaunawa a Arewa tsakanin Hausawa da Fulani, inda aka samu wani bangare na al’umma da ke ƙoƙarin raba daɗaɗɗen zumuncin da ke tsakanin waɗannan manyan ƙabilu na Arewa. Sakamakon halin tabararewar tsaro da ake fuskanta a wasu jihohin Arewa, inda wasu ke ganin, lokaci ya yi da Hausawa za su nisanta kansu daga ayyukan da wasu tsageru daga cikin Fulani ke aikatawa, wanda ke zubar da kimar al’ummar Arewa. Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana cewar, maganganun da ake yi na da nasaba da siyasa da wani buri da wasu ke son cimma na raba kan ’yan Arewa.
Harwayau kuma, taron ya duba irin gudunmawar da marubuta waƙoƙi na Hausa da Turanci ke bayarwa ga cigaban al’adu da zamantakewa, ta cikin kalmomi na hikima da basirar da Allah Ya basu. Marubuta waƙoƙi irin su Dakta Isma’il Bala, Nasiba Babale, Abdulbasit Abubakar Adam, da Salim Yunusa, sun bayyana yadda rubutattun waƙoƙi ke taka rawa wajen ilimantar da jama’a. Sun kuma ƙalubalanci matasa masu tasowa da hukumomi su mayar da hankali sosai wajen amfani da hikimomi don faɗakar da al’umma. Yayin da aka nemi gwamnati ta zuba jari sosai a cikin harkar fasaha da ƙirƙira, da aiki da dokar kare hakkin mallakar aikin basira da mutum ya ƙirƙiro. Yadda masu basirar rubuce-rubuce da waƙe-waƙe za su ƙara ba da himma wajen ba da tasu gudunmawar ga cigaban ƙasa, da taskance abubuwan da ake samarwa domin ’yan baya su amfana.
Akwai kuma batun gudunmawar mata a harkokin ilimi da fasaha, da rawar da ƙungiyoyin sakai na masu zaman kansu ke bayarwa ga cigaban zaman lafiya da sasanta tsakanin al’umma. Mun ji irin ƙoƙarin da ƙungiyoyi daban-daban ke bayarwa a matakai iri-iri don isa ga al’ummar da ke buƙatar kulawar su. Sannan an yi bitar wasu littattafai da suka haɗa da littafin da Farfesa Audee T. Giwa ya wallafa na baya-bayan nan mai suna ‘Zabba’u’. Da littafin da matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufa’i mai suna ‘An Abundance of Scorpions’. An kuma yi bitar littafin rubutattun waƙoƙin turanci na Dakta Isma’il Bala, wato ‘Ivory Night’. Mun ga irin gogewa da basirar jefa tambayoyi daga fasihan marubuta da mawaƙa, irinsu, Nasiba Babale, Ahmad Mubarak Tanimu, Abdulbasit Abubakar Adam, Aisha Indabawa da Aliyu Jalal.
Babu shakka taro ya yi armashi sosai. An yi musanyen ilimi da fahimta, an ƙara wa juna sani game da abinda ya shafi adabi, ilimin ƙirƙira da fasahar zamani. An kuma sada zumunci a tsakanin abokan hulɗa waɗanda aka saba da juna a baya, da waɗanda aka yi haɗuwar farko a Zariya. Sannan an shaƙata da waƙoƙin baka masu ma’ana da aka tsara su kan muhimmancin al’adu da tarbiyya, daga gwanayen masu sarrafa harshe irin su Faisal Ahmad Smith, Khalid Imam Khalid, Aisha Indabawa, Hidaya Mahmoud Muhammad, Khairat Omar, David Taiwo, Shafa’atu Muhammad, Harajnah Umar Ragada da sauransu. Yayin da Husayni Zaguru Abdulƙadir daga Abuja ya ƙayatar da jama’a da rawar sa da ya ɗauko salonta daga mutanen Turkiyya.
Bayan kammala taron, na samu zantawa da wasu daga cikin mahalarta taron kamar irin su Hajiya Hadiza El-Rufa’i matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, wacce ta yaba wa mai shirya taron, Maryam Shehu, bisa jajircewarta da ƙoƙarin da ta yi na haɗa wannan taron. Yayin da ta yi alƙawarin ba da gudunmawa don cigaba da raya wannan taro, ƙarƙashin gidauniyar ta. Ta ce, ‘Gaskiya na ga ƙoƙarin waɗannan matasa, na jinjina musu sosai. Yakamata a basu haɗin kai da goyon baya, ta yadda abin zai ƙara haaka yadda yakamata. Irin abubuwan da matasan nan suka yi abu ne da muke da buƙatar mu ga ya cigaba, saboda a samar wa matasan Arewa murya kuma a basu dama su nuna basirar su da abin da baiwarsu ta iya ƙirƙira, domin duniya ta san mu ma a Arewa muna da matasa masu basira. Ba wai kowanne lokaci aka tashi magana sai dai a kawo ’yan kudu ba.’
Shi ma Malam Abdulbasit Abubakar Adam daga Jihar Kano, ɗaya daga cikin jigogin taron cewa ya yi.’ Gwamnati na da muhimmiyar rawa da za ta taka don ganin cewa ta tallafawa ayyukan fasahohi na raya al’adu ta hanyar ƙirƙira. Abin farinciki ne yadda yanzu gwamnati ta fara fahimtar haka tunda har ma’aikata ta musamman ta kafa don raya al’ adu da cigaban fasahar ƙirƙira. Yana da kyau wannan ma’aikata ta kawo wasu shirye-shirye da za a taimakawa waɗanda ke kan wannan harka. Domin shi adabi da kuma ƙirƙira suna da muhimmanci sosai wajen jawo hankalin jama’a da fahimtar da su, ta hanyar wayar da kai cikin nishaɗi. Ba lallai sai akan batun tsaro kaɗai ba, akwai abubuwa da dama da harkar adabi da ƙirƙira za su taimakawa al’umma da hukumomi’.
Wata matashiya daga Jihar Yobe, Shamsiyya Ibrahim Barde ta nuna yabawarta da jindaɗin kasancewa a Zariya, da nufin halartar wannan taro, wanda ta ce ta ƙaru sosai daga abubuwan da aka tattauna. Ta ce, ‘A gaskiya taron nan ya ƙayatar da ni sosai. Idan da a ce za a riƙa shirya irin wannan taro a kowacce jiha a arewacin ƙasar nan, babu shakka za a ƙarfafa wa matasan marubuta da mawaƙa gwiwa. Sakamakon yadda ake da ƙarancin masu ƙarfafawa da dafawa irin waɗannan matasa a Arewa. A irin waɗannan taruka ne za su ga masu basira irin tasu, kuma har su gane suna da gudunmawar da za su bayar, wajen raya al’adunsu, samar da tsaro da zaman lafiya’.
Shi ma Abubakar Sani ɗan Bahaushe daga Jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar NorthBook, ya bayyana gamsuwarsa da yadda taron ya gudana. Yana mai cewa, ‘Babu shakka ko da ba a shirya wannan taro a ko’ina ba yakamata a shirya shi a Zariya, kasancewar nan ne birnin ilimi.
Sannan yadda taron ya mayar da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da suka shafi adabi da al’ umma, musamman tattaunawar da aka yi kan gudunmawar marubuta da harkokin adabi ga cigaban tsaro da zaman lafiya. Lallai ne ya zama jama’a na taimakawa gwamnati a ƙoƙarin da take yi na kawo cigaba a ƙasa. Kuma babu shakka hanyar amfani da fasahar zamani da ƙirƙira wajen shawo kan matsalolin tsaro da zaman lafiya na da muhimmanci sosai, a maimakon amfani da ƙarfi.
Asma’u Abubakar Musa, marubuciya ce kuma mai rubutun waƙen baka, daga Jihar Filato ta bayyana cewa, ‘Shirya irin waɗannan tarukan zai taimaka wa matasa sosai, musamman mata, wajen ba su damar baje-kolin fasahar su, da kuma gabatar da wata matsala da take damunsu gwargwadon wuraren da suka fito, su kuma kawo shawarwari na yadda za a yi maganinta. A irin waɗannan tarukan ya kamata masu faɗa a ji da gwamnati, su zuba jari sosai don bunƙasa ayyukan fasaha da ƙirƙira a arewacin Nijeriya da ma ƙasa bakiɗaya. Abin da Maryam Shehu ta yi a nan Zariya ya buɗewa mata ƙofa kan yadda za su cigaba da shirya irin waɗannan taruka a jihohin da suka fito’.
Taron ya samu halartar manyan malaman jami’o’i, manazarta, marubuta, masu waƙen baka da matasa masu fasahohi iri-iri, daga jihohin Arewa da dama.
