
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Babbar Kotun Jihar Kaduna ta umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta kawo mata tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i a zama na gaba.
Mai Shari’a Darius Khobo ne ya bayar da wannan umarni yayin da yake ɗage zaman zuwa ranar Talata bayan lauya mai kare El-Rufa’i da masu gurfanar da shi sun amince a ɗaga sauraron ƙarar.
Da yake jawabi, lauyan ICPC Ayodeleji Adelukpe (SAN) ya bayyana cewa masu kare wanda ake ƙara sun nemi a ɗaga zaman domin bai wa jagoran tawagar lauyoyin da ke kare El-Rufa’i, Paul Erokoro (SAN) damar samun halarta, wanda ya je taron rantsar da sababbin manyan lauyoyi masu darajar SAN a Kotun Ƙoli a Abuja. Ya bayyana cewa, ya nemi a cigaba da zaman a ranar Talata da misalin ƙarfe 10 na safe, amma Erokoro ya buƙaci a fara da rana bisa amincewar mai shari’ar.
Adelukpe ya kuma bayyana mamakin rashin ganin El-Rufa’i a zaman yana mai cewa saƙon da ya samu daga masu kare El-Rufa’i bai nuna cewa ba zai samu halarta ba. Ya shaida wa kotun cewa ya samu labarin cewa El-Rufa’i ba zai samu halartar ba ne saboda yana son ya yi nazari akan rahoton sakamakon lafiyarsa.
Bayan haka ne kotun ta ɗage zaman zuwa ranar Talata, sannan ta umarci ICPC da ta gabatar da El-Rufa’i a zama na gaba.
