Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matashin da ya kashe abokinsa saboda N100 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wata Babbar Kotun Jihar Zamfara ta yanke wa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa a kan Naira 100.

An gurfanar da Dahiru kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zargin kashe abokinsa Shamsu Ibrahim inda ya daɓa masa wuƙa har lahira a lokacin da suke faɗa da juna saboda Naira 100.

Da yake karanta hukuncin, Alƙalin Kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke Unguwar Dallatu a garin Gusau a Jihar Zamfara, ya gurfana a gaban kotu a shekarar 2017 bisa zargin kashe abokinsa Shamsu Ibrahim da wuƙa kan N100.

Mai shari’a Yusha’u ya ce bayan ya saurari ɓangarorin biyu ya yanke wa Anas hukuncin kisan ne biyo bayan kashe abokin nasa.

Ya ce, “Bayan na saurari dukkan ɓangarorin biyu, na yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wanda ake tuhuma (Anas Dahiru) kamar yadda yake ƙunshe a Sashi na 221 na kundin tsarin mulki”.

A wani labarin kuma, alƙalin kotun ya kuma yanke wa wani Sadiƙu Abubakar hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa laifin yunƙurin fashi da makami a Ƙaramar Hukumar Bungudu da ke jihar.

An yanke wa Sadiƙu hukuncin ɗaurin-rai-da-rai bayan samunsa da hannu dumu-dumu wajen aikata fashi da makami ga wani ɗan kasuwa a ƙauyen Runji da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu wanda ɗan kasuwar ya damƙe shi ya kuma miƙa wa mahukunta.

Mai shari’a Mukhtar Yusha’u ya ce da ya ji ta bakin ɓangarorin biyu da shari’ar ta shafa, ya yanke wa Sadiƙu Abubakar hukuncin ɗaurin-rai-da-rai a ƙarƙashin Sashe na 221 na kundin doka.