
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta jaddada hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, wanda ya haramta ta wa Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa da aka fi sani da VIO, dakatarwa, karɓewa ko ƙaƙaba tara ga masu motoci.
A wani hukunci na tawagar alƙalai uku, kotun ta yanke hukuncin haramta ababe ukun da aka lissafo ga hukumar.
Da yake gabatar da shari’ar, Mai Shari’a Oyejoju Oyewumi ya ce ɗaukaka ƙara akan batun ba shi da nagarta.
Don haka ya yanke hukuncin tara ga ɓangaren da ya shigar da ƙarar (VIO) na Naira miliyan ɗaya da za biya wanda aka maka, wato ɗan gwagwarmayar kare ƴancin al’umma kuma Antonin ra’ayoyin jama’a, Abubakar Marshal.
Da fari Alƙali Nkeonye Maha na Babbar Kotun Tarayya ya ayyana cewa babu wata doka da ta ba VIO ikon dakatarwa, karɓewa ko tilasta wa masu ababen hawa biyan tara don kaɗai sun aikata wani laifi.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Marshal ya shigar da VIO ƙara kan abinda ya kira tauye masa ƴanci a yankin Jabi na birnin a ranar 12 ga watan Disambar 2023 daga jami’an VIO, lamarin da ya sa ya maka hukumar a Babbar Kotun.
