Kyaftin ɗin Super Eagles, Troost-Ekong ya yi murabus a hukumance

Spread the love

Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles, William Troost-Ekong, ya sanar da yin ritaya daga taka wa Nijeriya tamola.

Ekong mai shekara 32 ya sanar da matakin ne acikin wata sanarwa a shafukansa na sada zumunta kwana ɗaya bayan mai horarwa Eric Chelle ya zaɓe shi cikin tawagar farko ta ƴan wasan da za su wakilci Nijeriya a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2026.

“Lokaci ya yi da zan miƙa damar, na miƙa ƙyallen kyaftin ɗin,” inji shi. “A yau, ina sanar da yin ritaya daga taka leda a matakin ƙasa da ƙasa.”

Ekong bayan ya buga wa Super Eagles wasa 83 tare da cin ƙwallo takwas cikin shekara 10, shi ne ɗan wasa mafi hazaƙa a gasar AFCON ta 2023 da aka yi a Ivory Coast, inda Nijeriya ta ƙare a mataki na biyu.

A watan Agustan 2024 ne Ekong ya koma taka wa ƙungiyar Al-Kholood ta Saudiyya leda daga PAOK ta ƙasar Girka.

By Babaji