
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban jagoran Kiristocin Sakkwato, Bishop Matthew Hassan Kukah, ya ce cigaba da mallakar makami ga al’ummar da ke rayuwa a wurare masu fama da rashin tsaro ba mafita ba ne ga matsalar rashin tsaro a Nijeriya.
Bishop Kukah ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a Abuja yayin zaman tattauna muhimman al’amuran ƙasa da aka yi wa take da ‘A Whole-of-Society Approach to Prevention of Violence and Conflict in Northern Nigeria’.
Cibiyar kwamitin zaman lafiya ta Kukah da Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) ne suka shirya zaman.
Kalaman babban jagoran Kiristocin na zuwa ne yayin da wasu ƴan Nijeriya ke ta kiraye-kirayen bada damar mallakar makamai ga ɗaiɗaikun al’umma da kuma buƙatar haka da Majalisar Dattawa ke neman sanyawa a doka domin ba kai kariya akan taɓarɓarewar al’amuran tsaro a sassan ƙasar musamman ta arewaci.
Ya yi ƙalubalen abinda zai faru da makaman da aka ba mutane damar mallaka na su kare kansu muddin zaman lafiya ya dawo wa ƙasar.
Ya ƙara da cewa, Nijeriya tana da kasawa na rashin ƙarfin gidaje, rarrabuwar garuruwa, rashin gogewa tun daga tushe acikin al’umma, dalilan da a cewarsa ke bada damar ayyukan ƴan bindiga da sauran manyan laifuka a ƙasar.
Saidai duk da haka, ya ce Nijeriya za ta fita daga halin rashin tsaro ne yayin da ta iya kawo ƙarshen ƙalubalen al’amarin ta yadda kowane ɗan ƙasa daga kowane addini ko ƙabila zai haɗu da ɗan uwansa wajen yaƙar masu haddasa fitinar.

