
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hauwa Yilwa, ta yanke wa Safiya Salihu da Halima Abdullahi, wato mahaifiya da ƙanwar marigayi Kachalla Ibrahim Battujo, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan sun amsa laifukan da ake tuhumarsu a kansu.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama su ne bayan bincike ya nuna suna karɓar kuɗaɗe daga Battujo tare da taimaka masa da wasu bayanai da ake zargin sun taimaka wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Bayan amsa laifukansu a gaban kotu, Alƙalin ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 20, wanda da fari 40 ne akan amsa hannu a laifuka biyu.
Marigayi Battujo na daga cikin jagororin ‘yan bindiga da suka shahara a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, kafin jami’an tsaro su kashe shi a wani samame da aka kai a dajin Obajana da ke Jihar Kogi.
Wannan hukunci na nuna cewa doka ba ta tsaya kan masu aikata laifi kai tsaye kawai ba, har ma da duk wanda aka samu yana taimaka musu wajen aiwatar da miyagun laifuka acikin al’umma.
