Koyar da ɗalibai da harshen Hausa zai magance matsalar ilimi a Kano – Munzali Jibril

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Fitaccen masani kuma malamin harshen Turanci Farfesa Munzali Jibril ya ce koyar da ɗalibai da harshen Hausa shi ne kaɗai mafita ga matsalar ilimi a Arewacin ƙasar nan.

Munzali Jibril ya bayyana hakan ne yayin taron wuni ɗaya da ilahirin ‘yan takarar gwamna a mabanbantan jam’iyyu domin gabatar musu da manufofin da za su ciyar da Kano da Jigawa gaba.

Taron wanda Zauren Ƙwararru na Kano da Jigawa wato (Kano Jigawa Professional Forum) ya shirya da manufar kawo gyara kan yadda ake tafiyar da al’amura a jihohin biyu.

Farfesa Munzali ya ce ɗalibai da dama na da hazaƙa da za su iya karatu mai zurfi amma rashin kyakkyawan turanci na daƙile su.

Ya ce tun da dai karatun firamare da na ƙaramar sakandire na hannun gwamnatocin jihohi to ya kamata su sauya tsarin.

Kazalika ya ce: “A yanzu ɗalibi zai gama makaranta ya kuma samu sakamako amma da za a sanya shi ya rubuta layi ɗaya na turanci ba zai iya ba.”

A don haka ya ce zauren yana bada shawara ga masu ruwa da tsaki da su mayar da harshen uwa wanda za a dinga amfani da shi a makarantun firamare da na qaramar sakandire.

Da yake nasa jawabin ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamnan Kano kuma mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya ce matuƙar ya samu nasara to ba shakka zai yi amfani da shawarwarin da zauren ya bayar.

A cewarsa ba qaramin tunani aka yi ba wajen fitar da tsare-tsaren da ake ganin za su ciyar da Kano gaba.

Sannan ya yi kira ga dukkanin ‘yan takara da su sanya Kano a farko kafin akan duk wata buqata ta su ta ƙashin kansu.

Taron ya samu halartar ƙwarurru daga fannoni daban-dadan da ‘yan takarkaru da suka haxa da: Ɗan takarar Mataimakin Gwamna a APC Alhaji Murtala Sulen Garo, da na NNPP Alhaji Abba kabir Yusuf da matimakinsa Kwamared Abdulsalam da na PRP Salihu Tanko Yakasai da matimakinsa da na SDP Alhaji Bala Gwagwarwa da matimakinsa da ɗan takarar Sanata a NNPP Hon.

Abdurahman Kawu Sumaila da dukkanin ‘yan takara na jam’iyyun ƙasar nan.