Matsin rayuwa ya tilasta min sakin matata, inji wani magidanci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wani magidanci Amiru Sani mai kimanin shekara 27 a duniya ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewar ya saki uwargidansa saboda yanayin matsin rayuwa da ya shiga.

Magidancin mai mata biyu ya bayyana cewar yana matuƙar son matar tasa amma saboda matsin tattalin arziki da ya shiga ba zai iya cigaba da ɗaukar nauyinta ba.

“Ba don ba na sonta ba, ba don na gaji da zama da ita ba, na saketa ne kawai don samar wa kaina sauƙi daga halin tsadar rayuwar nan da muka samu kanmu a ciki,” inji shi.

Amiru Sani ya shaida wa majiyar Manhaja cewa ya saki uwargidansa a lokacin da yake neman mafita kan matsin tattalin arzikin da ya shiga sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Mutane da dama ne a ƙasar nan musamman masu ƙaramin ƙarfi ke kokawa bisa hauhawar farashin kayan masarufi wanda dalilai da dama su ka janyo kama daga karayar tattalin arziƙi, rashin ingantaccen tsarin taimakawa al’umma rage raɗaɗin talauci daga ɓangaren gwamnatoci da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *