‘Yan sanda sun ceto ɗan takarar majalisar dokoki daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar kuɓutar da ɗan takarar majalisar dokoki ta jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP a zaɓe mai zuwa na shekara ta 2023.

‘Yan bindigar dai sun yi garkuwa da Hon. Ibrahim Tafashiya wanda ke neman zama ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kankiya a zaɓe mai zuwa.

Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar.

“Gaskiya ne tawagarmu ta kuɓutar da Tafashiya daga hannun ‘yan ta’adda kuma an sake haɗa shi da iyalansa,” inji shi.

Kakakin rundunar ya ci gaba da cewa samun kiran gaggawa ke da wuya sai DPO na ƙaramar hukumar Kankiya Ilyasu Ibrahim ya haɗa jami’an ‘yan sanda ya kuma jagorance su zuwa hanyoyin da ɓarayin za su bi su ka kuma toshe hanyoyin.

Bayan musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu rundunar ta samu nasarar kuɓutar da Hon. Tafashiya.

Haka zalika ‘yan sandan sun kuma kuɓutar da magatakardar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita dake Dutsinma.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da magatakardan Kwalejin Ilmi a daren ranar Asabar a gidan sa.

‘Yan bindiga sun shiga gidansa sun sace shi, amma an samu nasarar ceto shi da misalin ƙarfe 1:00 na dare, jim kaɗan bayan sace shi daga gidansa.

Sai dai rundunar ba tai ƙarin haske ba akan yadda aka kuɓutar da shi daga hannun ɓarayin dajin.

A wani labari mai kama da wannan wasu ‘ yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku a garin Sabuwar Kwata dake ƙaramar hukumar Jibiya a Jihar Katsina.

Lamarin ya faru da asubahin ranar Litinin kamar yadda majiyar Manhaja ta samu.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoton rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ba tai ƙarin haske akan lamarin ba.