Sarkin Hausawan Pantami ya zama Jakadan Zaman Lafiya

Manhaja logo

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Wasu ƙungiyoyin al’umma uku a Gombe sun karrama Malam Abdussalam Muhammad Sarkin Hausawan Pantami da lambar yabo ta Jakadan Zaman Lafiya wato ‘Peace Ambassador’ a turance.

Ƙungiyoyin su ne Arewarmu Duniyarmu da Arewa Youth and Women for Change da kuma Hausa Fulani Youth and Development Orientation Forum Association of Nigeria (HAFYDOF).

Sun karramma Sarkin Hausawan ne a matsayinsa na dattijo mai kishin al’ummarsa da kuma taimaka wa matasa.

Da yake jawabi a wajen bikin da suka shirya a Gombe, Shugaban Ƙungiyar Zauren Hausawa ta duniya, Ambasada Muhammad Kabiru Kuri, ya ce sun karrama sarkin ne tun a ranar 26 ga watan Agusta a wajen taron shekara na ranar Hausawa ta duniya da ya gudana a garin Kano, amma bisa wasu dalilai da suka sa bai samu zuwa ba shi ya sa suka shirya bikin karrama shi a Gombe.

Kabiru Kuri, ya ce Malam Abdussalam Muhammad Sarkin Hausawan Pantami, dattijo ne da ya taka rawa sosai wajen ganin an haɗa kan Hausawa a Gombe, sannan kuma ya zama uba a Ƙungiyar Zauren Hausawa.

Ya kuma ce dattijon jajirtacce ne wanda duk irin amanar da aka ɗora masa yana saukewa ba tare da an same shi da rashin gaskiya ba, wanda ganin hakan ya sa ƙungiyoyi uku suka haɗu suka karrama shi.
Sannan ya ce karrama Sarkin Hausawan Pantami, da lambar yabo zauren al’ummar Hausawan duniya aka karrama domin daraja da dattakun ɗan su ne ya jawo aka karrama shi.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar Arewarmu Duniyarmu na ƙasa wanda har ila yau shi ne Sarkin Hausawan Tukulma, Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce al’ummar Hausawan Jihar Gombe ne suka zaɓo Sarkin Hausawan Pantami don a karrama shi bisa dattaku da ƙoƙarinsa.

Alhaji Ibrahim Haruna, ya ƙara da cewa duk wata fitina idan ta taso ko aka samu wata matsala idan suka tura shi a matsayinsa na dattijo zai shawo kanta.

A cewarsa ci gaban da Sarkin Hausawan Pantami ya samar musamman wajen daidaita sahun matasa abun a yaba masa ne wanda ganin hakan ya sa suka ba shi lambar yabo ta Jakadan Zaman Lafiya.

Daga nan sai ya ce bisa irin haɗin kan da suke samu yanzu suna ƙoƙarin haɗe kan ƙungiyoyin Arewa zuwa waje guda dan ƙara ciyar da yankin Arewa gaba ba tare da bambancin yare ko ƙabila ba, da idan aka samu nasarar hakan hatta matsalar garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya za a daƙile shi.

A nasa tsokaci shugaban ƙungiyar HAFYDOF na Jihar Gombe Kwamred Aliyu Muhammad Magayaki, ya ce sun karrama dattijon ne saboda a matsayinsu na matasa yana kula da su kuma ya basu shawarwarin da take kai su ga tudun mun tsira.

Aliyu, ya ce duk lokacin da suka zauna da Sarkin Hausawan Pantami, suna kula da shi wajen ganin bai da burin da ya wuce ya ja matasa a jiki ya basu shawarar da za ta taimakesu a rayuwa.

A don haka sai ya yi kira ga matasa musamman Hausawa da ƙungiyoyin al’umma wajen ganin sun yi koyi da abunda suka yi na zaƙulo dattawa a lungu da saƙo don karrama su.

A jawabinsa na godiya Sarkin Hausawan Pantami Malam Abdussalam Muhammad, godewa dukkan ƙungiyoyin ya yi wajen yaba musu bisa zaƙulo shi da suka yi suka ba shi lambar karramawa ta Jakadan Zaman Lafiya.

Sarkin Hausawan Pantami, ya ce bai da bakin gode musu amma hakan wani nauyi aka ƙara ɗora masa na ci gaba da jagorancin da yake yi, “ba zan fasa ba sai randa na koma ga Allah,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *