Ku na sharhin majalisa tamkar gardamar Messi da Ronaldo – Akpabio ga ’yan Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Majalisar Dattijawa, Godswill Akpabio, ya yi suka ga waɗanda ke yin sharhi kan al’amuran majalisa kan damɓarwar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Shugaban majalisar ya kwatanta muhawarar ‘yan ƙasar nan kan batun da magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, wanda ba su san abin da su ke magana a kai ba.

Akpabio ya yi wannan magana ne lokacin da ya karɓi wata tawaga ta shugabannin matasa daga yankin Neja Delta. 

Ya nuna damuwarsa game da abin da ya kira “muhawarar jama’a ba tare da sani ba” kan al’amuran da ke gudana a cikin majalisa.

Akpabio ya ce, hukuncin majalisa na dakatar da Natasha ya yi daidai da dokokin majalisar da tsarin ladabtarwasu.

Ya ce, “Ya kamata ku tafi ku bincika gaskiyar lamarin kafin ku fara yin sharhi a talabijin.”

“Idan ba ku karanta baibul ko kuma ba ku da alaƙa da Kiristanci, ba za ku iya yin ikirarin sanin abin da ya ke cewa ba. Haka ma, idan ba limamai ba ne, ba za ku iya fatawa da ayoyin Al-Kur’ani ba.”

“A amma kuna ganin wasu mutane da ba su da cikakken ilimi suna zaune suna yin sharhi kamar yadda ake yi a wasan ƙwallon ƙafa, suna cewa, ‘Ronaldo ya kamata ya buga ƙwallon nan daga hagu’.”

Shugaban majalisar dattawa ya ce, majalisar na da nasu tsarin warware matsaloli, yana mai cewa batun dakatarwar Natasha Akpoti-Uduaghan yana bisa tsari.

Ya ce, “Idan mutane ba su da cikakken ilimi game da hanyoyin da ake bi amma suka fara muhawara kan sharuɗɗan da ba su fahimta ba, wani lokaci, wannan abu yana damuna.”

“Don haka muna ba da shawara ga jama’a da su daina yin sharhi kan abubuwan da ba su sani ba, suna kuskure wajen fassara dokokin majalisa.”