Yadda Tinubu ya sasanta rikicin majalisar dokokin Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya warware rikicin shugabanci a Majalisar Dokokin jihar Legas inda ya amince Mudashiru Obasa ya ci gaba da zama shugaban majalisar.

Shugaban ya gana da Obasa da wasu ‘yan majalisar da suka fusata a wata ganawar sirri a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Bayan kammala taron, an ga ‘yan majalisar na rera waƙa cikin murna da cewa “A bisa umarninka za mu tsaya” tare da jinjina wa shugaban yayin da ya ke gudanar da al’amura a ofishinsa.

A cewar ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci taron, “an warware komai”.

Yayin da sanarwar a hukumance har yanzu ba ta fito ba, an tattaro cewa Tinubu ya dage cewa Obasa ya ci gaba da zama shugaban majalisar tare da gargaɗin cewa ya tafi da takwarorinsa.

An kuma ce, shugaban ƙasar ya umarci Obasa da ya janye ƙarar da ya shigar a kotu.

Rikicin shugabanci a majalisar ya ɗauki wani salo na daban a ranar 13 ga watan Janairun 2025, lokacin da aka tsige Obasa a matsayin kakakin majalisar Legas da sama da kashi biyu bisa uku na mambobi 40, wadanda suka kaɗa ƙuri’a kan rashin ɗa’a da kuma laifuka daban-daban.

Nan take aka zaɓi mataimakiyar Obasa a lokacin, Meranda, a matsayin sabon kakakin majalisar, inda ta zama mace ta farko da ta karɓi ragamar hukumar a jihar Kudu-maso-Yamma.

Obasa ya ƙi amincewa da tsige shi da kakkausar murya, yana mai ikirarin cewa hakan ya faru ne a lokacin da ba ya nan, a lokacin da ba ya Nijeriya.

Sai dai ‘yan majalisa 36 da ke biyayya ga Meranda sun dage cewa tsige Obasa shi ne na ƙarshe kuma Merenda ta ci gaba da zama shugabar majalisar.

Bayan shafe makwanni ana taaaddamar shugabanci, Obasa mai wakiltar mazaɓar Agege na ɗaya, Mudashiru Obasa, a ranar 3 ga watan Maris aka sake zaɓensa a matsayin shugaban majalisar mai wakilai 40.

An sake zaɓensa ne bayan murabus cin Mojisola Meranda wadda fa sauka daga muƙamin shugabancin majalisar.

Meranda, wacce ke wakiltar mazaɓar Apapa I, ta sanar da murabus cin ta a zauren majalisar, inda nan take ‘yan majalisar suka sake zaɓar ta a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar.

‘Yan majalisar sun yaba wa salon shugabancinta da kuma samar da zaman lafiya a majalisar dokokin jihar Legas. Sun kuma yaba wa ƙarfinta da tawali’u bisa bin ƙa’idojin jam’iyyar APC.

By ukarofi