Daga BASHIR ISAH
Muƙƙadashin Babban Sufeton ‘Yan Sanda, IGP Olukayode Egbetokun, ya bai wa ma’aikatan kula da lafiya a faɗin ƙasa umarni a kan su riƙa yi wa duk wani da aka kawo asibiti ɗauke da raunin bindiga magani ba tare da neman rahoton ‘yan sanda ba.
Egbetokun ya ba da wannan unarnin ne tare kuma da kiran ma’aikatan kiwon lafiya da su wayar da kan ‘yan kan wannan batu.
IGP ya ba da umarnin ne bisa la’akari da Dokar wajabta kula da masu ɗauke da raunin bindiga ta 2017.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwar cikin gida mai ɗauke da kwanan wata 25 ga 2023 da kuma sa hannun babban jami’in rundunar, Olatunji Disu.
An tura sanarwar ne zuwa ga ɗaukacin Mataimakan da Kwamishinonin ‘Yan Sanda da kuma shugabannin kwalejojin ‘yan sanda a Ikeja da Kaduna da Oji-River da Maiduguri da kuma Enugu.
