Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya shawarci ’yan NIjeriya da su zaɓi shugabanni nagari a zaɓe mai zuwa ba tare da la’akari da ’yan jam’iyya ba.
Ya bayyana haka ne a wajen taron al’umma na ƙasa karo na 27 da Cibiyar Musulunci ta ƙasa ta shirya, wanda aka gudanar a sansanin Sultan Sa’ad Abubakar Hajj Camp da ke Bauchi.
Tsohon Gwamnan wanda ya ce ƙalubalen da al’ummar Musulmi ke fuskanta abu ne mai wuyar gaske, yayin da ya shawarci ‘yan Nijeriya da su zaɓi mutanen da suka tabbatar da gaskiya a lokacin zaɓe.
“Ina ba da shawarar cewa mutane su zaɓi shugabanni nagari ko da sun fito ne daga jam’iyyar shaiɗanu ne”.
A nasa ɓangaren shugaban al’ummar Musulmi na ƙasa Farfesa Muhammad Babangida Muhammad wanda ya bayyana cewa an kafa Cibiyar Musulunci ta ƙasa ta Zariya a shekarar 1980 a matsayin wata riga ta ƙungiyar al’umma da ‘ya’yan ƙungiyar ɗalibai Musulmi da ke son ci gaba da yi wa al’ummarsu hidima bayan kammala makaranta.
Mohammed ya ce, a cikin shekaru 50 da suka wuce, al’ummar Musulmi sun inganta haɗin kai, kyakkyawan shugabanci da haɗin kan ƙasa.
Akan harkokin tsaron ƙasa, shugaban ƙungiyar Umma ta ƙasa ya bayyana damuwarsa kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.
“Ya kamata gwamnatoci a kowane mataki su ba da fifiko kan aikin noma da sanin makamar aiki don daƙile shigar matasa ayyukan aikata laifuka”.
