Daga DAUDA USMAN a Legas
Kungiyar Wala Warabe Dure ta al’ummar ƙaramar Hukumar Gwoza da ke jihar Borno, mazauna jihar Legas, ta gudanar da babban taron sada zumunta da ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta a jihar.
An gudanar da taron ne a ranar Lahadin da ta gabata a yankin Marine Bridge da ke ƙaramar hukumar Apapa a jihar Legas, inda dumbin shugabanni, mambobi da matasan ƙaramar hukumar Gwoza mazauna sassa daban-daban na Legas suka halarta.
Taron ya mayar da hankali ne kan bunƙasa haɗin kai, taimakon juna da kuma samar da hanyoyin da za su ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban al’ummar Gwoza da jihar Borno baki ɗaya a Legas.
A yayin taron, mahalarta sun gabatar da jawabai daban-daban tare da bayar da shawarwari kan yadda ƙungiyar za ta ci gaba da kare martaba da mutuncin ’yan asalin Gwoza da Borno da ke zaune a jihar Legas.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ƙungiyar na jihar Legas, Umar Bello, ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin haɗa kan ’yan asalin Gwoza da jihar Borno da kuma sauran ’yan Arewa mazauna Legas, ta hanyar taimakon juna a lokutan buƙata.
Ya ce, sau da dama mutane kan shigo Legas domin neman na kai, amma ba su san kowa ba, lamarin da ke jefa wasu cikin matsaloli musamman wajen neman aikin yi da rayuwar yau da kullum.
A cewarsa, idan ƙungiyar ta gano cewa mutum nagari ne kuma mai gaskiya, za ta tallafa masa ta hanyoyi daban-daban domin samun mafita.
Haka kuma ya ce idan wani daga cikin mambobin ƙungiyar ya samu matsalar rashin lafiya, hidimar aure, suna, ko wata matsala ta rayuwa da ta dace, ƙungiyar za ta shiga gaba wajen taimaka masa.
Shugaban ƙungiyar ya kuma ja hankalin ’yan asalin Gwoza, jihar Borno da sauran al’ummar Arewa mazauna Legas da su ci gaba da zaman lafiya tare da sauran ƙabilun da suke rayuwa tare da su a jihar.
Ya buƙace su da su kasance masu bin dokokin gwamnatin jihar Legas tare da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo matsala ko karya doka.
A ƙarshe, Umar Bello ya yaba wa gwamnatin jihar Borno bisa ƙoƙarin da take yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
