Kuntau Science Academy ta yi bikin yaye ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI a Kano

A ranar Asabar ɗin da ta gaba ne, shahararriyar makarantar nan ta Kuntau Science Academy (KSA) reshen court road, ta yi bikin yaye ɗalibanta waɗanda suka kammala sakandare, wasu firamare wasu kuma ƙaramar sakandare, a watan Agustan shekarar da muke ciki ta 2021.

Taron wanda aka gudanar da shi a dandalin kasuwar baje koli da ke titin gidan Zoo, an shirya shi ne a ƙarƙashin shugabancin shugaban rukunin makarantun Kuntau, Farfesa Mustafa Karkarna.
 
Taron ya samu halartar manya mutane, da iyayen yara da kuma shugabannin gudanarwa na rukunin makarantun Kuntau daban-daban da suke birjik a jahar Kano.

Shugabar makarantar Kuntau reshen unguwar Court road, Hajiya Jamila Mustafa, ta nuna farincikinta da yadda iyayen yaran makaranta da malamanta a kan irin yadda suka ba da gudunmowa wajen tabbatar da nasarar taron.

Hajiya Jamila ta ƙara da cewa,  za ta yi amfani da wannan dama domin  mi}a saƙon godiyarta ga iyayen wasu yara guda uku: Farhana Mahmud, Hauwa Datti da Fatima Mahammad wajen jajircewa da suka yi suka amince waɗannan yara nasu suka tafi ƙasar Amurka domin wakiltar Makarantarsu da Jahar Kano a wata gasa. Abinda ta kira da namijin ƙoƙari.

Shugabar Makarantar Kuntau reshen courtroad tare da wasu mahalarta taron yaye ɗaliban da makarantar ta shirya

Domin a cewarta, ba wannan ne karo na farko da ɗaliban wannan makarantar suka samu irin wannan ta yi na fita ƙasashen ƙetare don yin gasa ba. Amma sai iyayensu su hana su. A don haka ta ce, ta jinjina wa waɗannan iyaye. 

A karshe, shugabar makarantar ta bayyana cewa, makarantar ta yi alƙawarin ba da tallafin ci gaba da karatu ga wasu ɗalibai da suka zama zakaru a azuzuwansu domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa da su da iyayensu.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da makarantar Kuntau reshen Court road take shirya irin wannan taro don yaye ɗalibanta.