Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jamilu Chiroma ta rantsar da sabbin ɗalibai

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jamilu Chiroma da ke Kano ta gudanar da bikin rantsar da sabbin ɗaliban da aka ɗauka domin fara karatu a makarantar.

An gudanar da bikin ne a harabar kwalejin da ke kan titin Airport a Kano, ranar Asabar, tare da halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban, iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Da yake jawabi bayan rantsar da ɗaliban, wanda ya assasa kwalejin, Alhaji Jamilu Abubakar Chiroma, ya bayyana cewa makarantar na daga cikin cibiyoyin ilimi biyar da suka samu sahalewar Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa domin gudanar da shirye-shiryen Diploma na ƙasa (ND) da Higher National Diploma (HND).

Ya ce yanzu haka kwalejin na cikin tsarin JAMB Portal kamar sauran jami’o’i, sannan tana da sahalewa daga Ma’aikatar Lafiya ta ƙasa da kuma ta Jihar Kano domin gudanar da karatun fannin lafiya.

A cewarsa, makarantar na aiki tuƙuru wajen bunƙasa harkar ilimi da kuma cimma burin kafa jami’a mai zaman kanta a jihar Kano nan gaba.

Jamilu Chiroma ya yi ƙarin haske kan yadda aka kafa kwalejin, inda ya bayyana cewa an fara ne da koyar da yara darussan Turanci da Lissafi a unguwar Kwana Huɗu da ke ƙaura Goje, kafin daga bisani aka mayar da hankali kan koyar da Lissafi da sauran darussan kimiyya.

Ya ce daga wannan yunƙuri ne aka kafa cibiyar koyar da Kimiyya da Lissafi, wanda daga bisani ya haifar da kafa kwalejin lafiya da fasaha.

A cewarsa, a shekarar 2022 ne makarantar ta samu sahalewa daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, yayin da a shekarar 2025 ta samu damar shiga tsarin JAMB Portal tare da samun sahalewar Ma’aikatar Ilimi.

Ya ƙara da cewa duk da cewa kwalejin ba ta daɗe da kafuwa ba, ta riga ta gudanar da jarabawar Council sau biyu tare da samun sahalewa daga WAHEB.

Chiroma ya bayyana cewa makarantar na shirin fara yaye ɗalibai daga shekarar 2026 zuwa 2027 a fannoni irin su Dental Surgery Technician, Community Health da Public Health.

Ya kuma bayyana cewa kwalejin na da ɗalibai sama da 500 a fannoni daban-daban, tare da tabbatar da cewa ana ba su ingantaccen ilimi da ƙwarewar aiki kafin kammala karatunsu.

A cewarsa, makarantar na da ingantaccen dakin gwaje-gwaje na kimiyyar lafiya tare da kayan aiki na zamani, yayin da kuɗaɗen makarantar kuma suke da sauƙi domin bai wa iyaye damar biyan kuɗin karatu cikin sassauci.

Haka kuma ya ce makarantar na bai wa ɗalibai tarbiyya ta gari da koyarwar addinin Musulunci, tare da ware maza da mata a azuzuwa domin tabbatar da kyakkyawan yanayin karatu.

Ya ƙara da cewa ana kai ɗalibai asibitoci domin samun ƙwarewar aiki a aikace tare da koyar da muhimmancin tsafta da kula da lafiya.

Alhaji Jamilu Abubakar Chiroma ya bayyana cewa sama da sabbin ɗalibai 200 aka rantsar a wannan karo daga fannoni daban-daban da suka haɗa da Public Health, Health Promotion, Community Health da Dental Health.

By ukarofi