Kwalejin Shari’ah ta Aminu Kano ta cika shekara 50 — Jakada

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI, D/Kudu

Kwalejin Addinin Musulunci da Shari’ah ta Aminu Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) ta cika shekara 50 da kafuwa, inda aka samu gagarumar nasara da ci gaba musamman a fannin shari’ah a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Shugaban kwalejin, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai bayan ƙaddamar da shirin bikin cikar kwalejin shekaru 50, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Abdullahi Umar Ganduje da ke harabar makarantar.

Jakada ya ce kwalejin ta yaye manyan alkalai, lauyoyi, limaman Juma’a da ma’aikatan kotuna waɗanda ƙasar nan ke alfahari da su. Ya ƙara da cewa makarantar ta taka muhimmiyar rawa wajen cike gibi a fannin shari’ah.

Ya bayyana cewa an shirya bikin ne domin tunawa da irin gudunmawar da kwalejin ta bayar, da kuma haskaka nasarorin da aka samu tare da duba ƙalubalen da ake fuskanta domin nemo mafita.

A cewarsa, tun da ya zama shugaban kwalejin — wanda shi ne mafi daɗewa a kujerar — an samu gagarumin ci gaba, ciki har da samar da karatun digiri ta hanyar haɗin gwiwa da Jami’ar Tarayya da ke Dutse, da dawo da wasu shirye-shiryen diploma da kuma ƙirƙirar sabbin fannonin karatu.

Ya kuma ce an samu ci gaba a bangaren gine-gine, inda aka gina sabbin ajujuwa, aka gyara tsofaffi, tare da gyaran babban masallacin kwalejin.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta ƙasa, Alhaji Mahmud Garba Kabuga, ya bayyana farin ciki kan cikar wannan rana, yana mai cewa kwalejin ta taka rawar gani wajen bunƙasa ilimin addini da shari’ah.

Kabuga ya kuma bayyana irin ayyukan da ƙungiyar ta gudanar, ciki har da gyaran rijiyoyi da bututun ruwa, wanda ya taimaka wajen magance matsalar ruwa a makarantar. Ya yi kira ga tsofaffin ɗalibai da masu hannu da shuni da su riƙa tallafawa makarantar.

By ukarofi