Daga JOHN D WADA a Lafia
A yayin da ake cigaba da bukukuwar ranar dimokuraɗiyya na shekarar 2026, kwamandan kare haɗura na ƙasa reshen jihar Nasarawa Yahaya Sabo Adikwu yayi kira na musamman ga al’ummar jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su tabbatar suna kiyaye dokokin kare hadura a manyan hanyoyi da suke amfani da su kafin lokaci da kuma bayan bukukuwan.
Kwamanda Yahaya Sabo Adikwu yayi kiran ne ta bakin mai magana da yawun hukumar John Nwankwo a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a ofishin sa da ke babban sakatariyar hukumar ranar Laraba.
Yace kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda ake samun ƙarin zirga-zirgan ababen hawa da ke kai komo.
Ya bayyana wasu daga cikin halaye da ke jawo haɗura a manyan hanyoyin jihar ta Nasarawa da ƙasa baki ɗaya cewa sun haɗa da rashin kiyaye dokoki da sharuɗan hanyoyi irin su gudun fitar hankali da yin lodi fiye da kima da over taking cikin ganganci da shan kayayyakin maye ana tuƙi da rashin kula da lafiyar ababen hawan kansu kamar tayu da birki da dai sauran su da dama.
Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Yahaya Sabo Adikwu ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin hukumar da sauran hukumomin dake tabbatar da kare haɗura a jihar Nasarawa kawo yanzu inda ya yaba wa haɗin kai da sauran hukumomin ke cigaba da bai wa hukumar nasa don tabbatar da cimma burin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta kare haɗura a manyan hanyoyin.
Har ila yau Yahaya Sabo Adikwu ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa jami’an sa dangane da yadda suke gudanar da ayyukan su yadda yakamata cikin tsari ta gudanar da gangamin wayar da kawunan al’umma cikin harshen turanci da Hausa a duka sassan jihar a ko yaushe inda ya ƙara da cewa zuwa yanzu da zuwan sa jihar ta Nasarawa a matsayin kwamandan hukumar hukumar ta samu ɗimbin nasarori da dama ta gudumawar jami’an nasu inda ya buƙace su da su cigaba da yin aiki tuƙuru.
