Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ɗan takarar majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Fagge a Jam’iyyar ADC, Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya jajentawa ‘yan kasuwar Kantin Kwari bisa iftila’i da ya samesu na ambaliyar ruwa da ya janwo lalacewar dukiya mai tarin yawa.
Wakili ya kuma yi irin wannan jaje ga ‘yan kasuwar Bairut suma bisa matsalar da aka samu a kasuwar ta rushewar wani gini da ya janwo asarar rai da raunata mutane.
Kwamared Haruna Wakili ya yi fatan waɗanda abin ya shafa Allah ya mayar musu da alheri ya kuma bunƙasa abinda aka rasa.
Ɗan majalisar dai ya yi irin wannan jaje ga al’ummar yankin ‘yan mata Gabas dake yankin Fagge bisa iftila’i na zaizayar ƙasa da ambaliyar ruwa ya shafe su da fatan Allah ya mayar musu da alkhairi ya kawo musu ɗauki na gaggawa kuma ya mayar da alkhairi ga dukkan al’umma da ambaliyar ruwan ya shafa.
Kwamared Haruna ya yi kira ga mahukunta akan su kai ɗauki don tallafa wa waɗanda suka yi asara sannan a ɗauki matakai don yin kandagarki ga aukuwar abin nan gaba.
Kwamared Haruna ya ce idan ya zama wakilin al’ummar Fagge a tarayya zai yi ƙoƙarin ɗaukar matakan ganin an kyautata yanayin magudanan ruwa da kuma kawo ɗauki ga matsalar zaizayar ƙasa a wasu sassan yankin.
