Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan ma’aikatar ilimin firamare da sakandare ta Jihar Katsina, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya duba yadda ake gudanar da jarabawar NECO da kuma ayyukan gina makarantu a yankin Daura.
A ziyarar, ya bibiyi jarabawar Chemistry ta NECO da ta gudana a wasu makarantu, ya kuma gana da shugabannin makarantu kan inganta koyarwa, sannan ya duba aikin gina Model Special Secondary School a Dumurkur da kuma ɗaya daga cikin sabbin makarantun sakandare 30 da gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ke ginawa.
Kwamishinan ya yaba da ingancin ayyukan tare da buƙatar masu aikin su kammala su cikin wa’adin da aka tsara.
Kwamishinan ya cigaba da rangadin makarantun firamare da na sakandire a jihar domin tabbatar da bunƙasar harkar Ilimi a jihar.
Ya bayyana jin daɗin sa kan yadda gwamna Dikko Raɗɗa ke ba harkar ilimi kulawa a jihar.
Mako biyu da suka wuce gwamnan Jihar ya ƙaddamar da sabbin malamai fiye da 2000 da gwamnati tare da haɗin gwiwar AGILE ta ɗauka, wanda a yanzu da hawan gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki malaman makarantun firamare da na sakandire fiye da 10000.
