Kwamishinan Jigawa ya musanta zargin lalata da matar da aure a Kano

Spread the love

Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman na Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, ya ƙaryata zargin da Hisbah ta Kano ta yi, inda ta ce yana da hulɗa da matar aure.

Wannan ya biyo bayan labarin zargin hulɗa da matar aure a cikin yanayi da bai dace ba wanda ya shafi Auwal Danladi Sankara, wanda ya bazu a kafafen yaɗa labarai daban-daban.

Auwal Sankara ya ce”An sanar da ni wani rahoton jarida a safiyar nan da ke zargin cewa ni, Auwal D. Sankara, Kwamishinan Ayyuka na Musamman a Gwamnatin Jihar Jigawa, an kama ni da Jami’an Hisbah na Jihar Kano da zargin yin hulɗa da matar aure.

“Ina so in bayyana ƙarara cewa waɗannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne, marasa tushe, kuma cike suke da mugunta, wanda aka yi niyya don ɓata sunana. Ina kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙirƙirarren labari da wasu ‘yan siyasa suka ƙirƙira domin ɓata mutuncina da ƙimata.

“Ni mijin aure ne, kuma ina daraja aure da dukkan mutuntawa. Ba zan taɓa aikata wani abu da zai keta mutuncin aure ba. Zan ci gaba da jajircewa wajen tsayawa kan ƙa’idodi da darajoji da nake tsayawa a kai.

“Ina daukar wannan batu da muhimmanci, kuma zan ɗauki matakin doka kan waɗanda suka yaɗa wannan ƙarya da kuma yunƙurin cutar da ni.”

By ukarofi