
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar gudanarwa ta babban Masallaci na Ƙasa da ke Abuja (National Mosque), ta naɗa Farfesa Iliyasu Usman a matsayin ɗaya daga cikin limaman masallacin.
Lamarin da ya sa ya zamo mutum na farko daga ƙabilar Igbo da ya samu matsayin limanci a masallacin.
Farfesan Larabcin zai zama mataimaki ga Farfesa Ibrahim Maƙari da kuma Farfesa Muhammad Kabir da kuma limami na huɗu, wato Sheikh Ahmad Onilewura.
Al’umma da dama musamman ƴan ƙungiyar musulman Kudu-maso-Gabas (SEMON) sun yi murnar samun labarin inda ƙungiyar ta yaba masa kan ƙoƙarin da ya ke yi ta fuskar shugabanci da hidimta wa addini.
Ƙungiyar ta kuma ce hakan dama ce ta ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin al’ummar Musulmin ƙabilar da sauran musulmai, ta na mai yi masa fatan alkhairi da sauke nauyin da Allah ya ɗora masa.
