Kwara: Ƙungiyar Shiya Development ta yi ƙorafin salon naɗin sarkin Masarautar Okuta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Shiya Development a Jihar Kwara, ta yi ƙorafin salon naɗin sarkin Masarautar Okuta da ke Ƙaramar Hukumar Baruten ga Hukumar kare ‘yancin ɗan-adam (NHRC).

A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024 ne aka samar da hanyoyin zaɓen sarkin gargajiya a yankin sakamakon samun gurbin hakan da aka yi. Saidai al’amarin ya samu tsaiko sakamakon rashin kiyaye ƙa’idojin da aka gindaya daga mambobin kwamitin zaɓen.

A wata takarda da Shugaban ƙungiyar, Yakubu Kio ya fitar, Shiya Development Association ta bayyana cewa al’ummar Okuta sun koka ganin yadda ɗan takarar da suka amince da shi bai samu muƙamin ba.

A cewarsa, an yi maguɗi wajen ɗaukar ɓangare a lokacin zaɓar wanda ake son bai wa sarautar, lamarin ya nemi tayar da rikici a ƙauyen.

Ya ce, bayan haka ne ‘yan sanda suka riƙa razana al’umma da kuma kama waɗanda suka bijire wa salon naɗin sarkin.

Ya bayyana cewa, sun yi yunƙurin wanda suka gabatar ya samu sarautar, amma hakan ya ci tura. Akan haka ne ƙungiyar ta yi ƙorafin matakin ga NHRC.

Saboda haka ne ƙungiyar ta yi kira ga NHRC da ta da tsoma baki a al’amarin domin ganin an bai wa zaɓin al’ummar yankin kujerar.

By Babaji