Ramadana: MOPPAN ta jinjina wa ‘yan Kannywood bisa tallafa wa al’umma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar masu Shirya finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) ta yaba wa wasu daga cikin jaruman finafinan bisa hoɓɓasa da suak yi wajen raba wa al’umma tallafin kayan abinci domin sauƙaƙa musu halin matsin rayuwa yakin azumin watan Ramadana.

A wata takarda da ta fitar a ranar Litinin ta hannun Sakataren, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel, MOPPAN ta ce jaruman sun yi abin da ake buƙata musamman ganin yadda malamai suke faɗakarwa akan falalar taimakon marasa galihu.

A cewar sanarwar, ababen da aka raba wa mabuƙatan sun haɗa da shinkafa, taliya, ababen hawa, tsabar kuɗi da dai sauransu.

MOPPAN ta kuma yi addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi tare da sanya aikin cikin mizani kyawawan ayyukansu.

Cikin waɗanda suka bayar da tallafin akwai Abdul Amart, Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Abba Al-Mustapha, Sani Danja da sauran waɗanda suka tallafa a ɓoye.

A ƙarshe, ƙungiyar ta kuma jaddada ta’aziyyarta bisa rasuwar Nura Shariff, wanda ma’aikataci ne a kamfanin Abnur Entertainment da ya rasu makonni kaɗan da suka gabata, kamar yadda sakataren ya bayyana a madadin shugaban MOPPAN, Shehu Hassan Kano.

By Babaji