Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mutanen da suka amfani da tallafin sun fito daga ƙananan hukumomi 11 na shiyar Katsina da ke mazaɓar ɗan majalisar.
Sanarwar ɗauke da sa hannun ɗaya daga cikin mataimaka na musamman kan yaɗa labarai malam Lawal Gwanda ya sanya, ƙungiyoyin ‘yan siyasa, malama,masu unguwanni,mata da musu buƙata na musamman suka amfana da tallafin shinkafar da tuni aka raba.
A jawabinsa Sanata Abdul’aziz Musa Yar’Adua wanda ya sami wakilcin Janaral Manajan na KASSAROMA, Manjo Yahaya Garba Rimi mai ritaya,yayi kira ga al’ummar mazaɓar sa da suyi amfani da wannan wannan wata mai alfarma su sanya jihar Katsina cikin addu’a na samun zaman lafiya.
Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan matakan da ya ɗauka na ɗorewar zaman lafiya a jihar Katsina.
Sanatan wanda tsohon kanal din Soja ne ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi ba dare ba rana wajen tabbatar da tsaro da yaƙar yan bindiga a jihar.
Ya ce a matsayin sa na shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattijai na ƙasa ya iyakan ƙoƙarin sa wajen kyautata aikin su na magance ta’addanci a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.
Yar’adua wanda aka fi sani da suna Abdu Soja ya tabbatar wa al’ummar mazaɓar sa cewa ba zai gajiya ba wajen inganta rayuwar su da samar da ababen more rayuwa.
