
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da saƙon ankararwa ga al’umma, inda ya yi gargaɗin yiwuwar aukuwar munanan hare-hare daga ‘yan ta’adda waɗanda ke harin ofisoshin Amurka da makaratu masu haɗaka da ƙasar a Nijeriya.
A wani rubutu da ya fitar a Abuja, ofishin jakadancin ya shawarci ‘yan Amurka da ke Nijeriya da su kula yayin kai ziyara a wuraren harkokin jakadancin Amurka da cibiyoyi masu alaƙa da ita.
Musamman saƙon ya fi mayar da hankali akan ofisoshin jakadancin Abuja da Legas, inda ya yi kira a gare su da kasance masu sanya ido da ƙara ƙarfafa matakan tsaro yayin tafiye-tafiye zuwa yankunan jihohin.
A cewar ofishin, akwai buƙatar ‘yan ƙasar su riƙa bambance hanyoyin da suke bi wajen tafiya daga gari zuwa gari domin kauce we bibiyar su cikin sauƙi da zama a ankare don rage matakin haɗari.
Haka kuma, an shawarce su da su riƙa yin basaja ta hanyar yin shiga ta masu ƙaramin ƙarfi a yayin da suke bainar jama’a, kauce wa taruka da gangami da kuma tattauna shirin tsaro da iyalansu.
Sauran shawarwarin sun haɗa da tabbatar da wayoyin hannu suna da caji a kodayaushe saboda buƙatar gaggawa da sanin wuraren tsira yayin shiga manyan gine-gine.
A cewarsa, duk da waɗannan gargaɗi da shawarwari, ofisoshin jakadancin manyan biranen biyu za su cigaba da gudanar da harkokinsu yadda aka saba.
