Labour ta buƙaci ƴan Najeriya su yi haƙuri da gwamnatoci gabannin fara biyan sabon albashi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi kira ga ƴan Najeriya da su kasance masu haƙuri yayin da gwamnatin tarayya ta gwamnatocin jihohi ke ƙoƙarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata.

A ranar 29 ga watan Yuli, 2024 ne Shugaba Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Najeriya bayan tattaunawa a lokuta mabanbanta da ƙungiyar ƙwadago game da ƙara albashin sakamakon halin tsadar rayuwa da al’umma ke ciki.

Kafin haka ne ƙungiyar ta yi gargaɗin shiga yajin aikin wata guda matuƙar gwamnatin ta ƙi amincewa da buƙatar da ta gabatar a madadin ma’aikatan.

A watan Yuni ne ƙungiyar ta gudanar da yajin aikin kwana 1 na gargaɗi wanda a sanadiyyar haka aka samu asarar Naira biliyan 148.8 a Najeriya.

Tun bayan amincewa da sabon tsarin albashin da Shugaba Tinubu ya yi, jihohi bakwai ne kaɗai su ka naɗa kwamitin kula da harkokin albashin waɗanda su ka haɗa da; Kano, Kwara, Ogun, Borno, Jigawa, Ondo da Abia.

By Babaji