‘
Daga UMAR GARBA a Katsina
Wani lamari dake ɗaukar hankalin al’uma a halin yanzu shine, sace wasu jarirai ‘yan biyu, ko kuma tagwaye, tare da mahaifiyarsu dake zaman jego.
Lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a ƙaramar hukumar Kurfi inda suka afka gidan Lilila Sama’ila, suka sace tagawayen mace da namiji masu makonni huɗu kacal da haihuwa.
Mazauna garin sun tabbatar wa Blueprint Manhaja cewa, bayan da ɓarayin suka yi garkuwa da tagwayen sun kuma shiga cikin gari inda su kai ta yin harbe harbe lamarin da ya sa al’uma suka shiga cikin halin razana da fargaba.
Sai dai daga baya iyalan waɗanda a kai garkuwar da su, sun ce, ɓarayin sun tuntuɓe su inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 15 kafin sakin matar da jariran nata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, a cewar shi an kama wani da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutanen.
“Muna matuƙar ƙoƙari don ganin an ceto su. Kawo yanzu dai an kama mutum ɗaya da hannu a lamarin. Har yanzu ana ci gaba da bincike.” Inji shi.
‘Yan bindiga na ci gaba da yin garkuwa da mutane a Jihar Katsina duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro, gwamnatin jiha da ta tarayya ke cewa su na yi don shawo kan matsalar.
