Lambar yabon Blueprint za ta ƙarfafa ayyukanmu na ci-gaba a Jigawa, inji Gwamna Namadi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karɓi lambar yabo ta Jaridar Blueprint ta 2025, ta gwarzon gwamna da ya yi fice a harkar Horon Kasafi da Ci-gaban Noma, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarfafa gwiwa ga ƙoƙarinsu na sarrafa dukiyar al’umma bisa kyakkyawan tsari da ci-gaban harkar noma.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Babban Sakatarensa na Musamman, Adamu M. Garun-Gabas mai kwanan wata 5 ga Agusta, 2026, yayin amsa saƙon jaridar kan sanar da shi a matsayin wanda ya samu kyautar.

Namadi ya nuna godiyarsa ga Blueprint bisa yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Jigawa wajen ciyar da harkar kasafi, tsayar da gaskiya da adalci da ci-gaban harkar noma mai ɗorewa gaba a jihar.

Ya ce, wannan kyauta za ta ƙarfafa wa gwamnatin nasa akan matakanta na samar da kyawawan tsare-tsare da shirye-shirye don shugabanci na gari, tallafa wa manoma, inganta lamuran samar da amfanin gona da bayar da gudunmawa ga tsaron abinci a matakin ƙasa.

Kazalika, Umar Namadi ya jinina wa Blueprint Newspapers Limited bisa gudunmawarta ga ci-gaban ƙasa da ƙoƙarin da take yi wajen ganowa da yaba wa shugabanci na gari kuma abin koyi ga wasu jagorori a sassan Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply