Lantarki: Nijeriya tana bin Nijar da Togo bashin Dala miliyan 14

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa kwastomomin ƙasashen duniya sun gaza biyan bashin wutar lantarkin da suka kai dala miliyan 14.19 a rubu’in farko na shekarar 2024.

A cewar rahoton NERC, babu ɗaya daga cikin abokan hulɗar ƙasa da ƙasa guda huɗu – ciki har da ƙasashe makwabta irin su Jamhuriyar Benin, Nijar, da Togo – da suka biya kuɗin wutar lantarkin da ake bin su.

Rahoton ya ce, “A farkon shekarar 2024, babu wani daga cikin abokan cinikin ƙasashen waje guda huɗu da Hukumar Kasuwa (MO) da ya biya bashin ake bin sa na dala miliyan 14.19 da MO ta ba su don ayyukan da aka yi a farkon 2024. Hakazalika, babu ko ɗaya daga cikin kwastomomin da ke cikin Nijeriya da ya biya wani biyan bashin da aka tara na N1,860.11 miliyan da MO ta ba su don ayyukan da aka yi a daidai wannan lokacin.”

Rahoton ya kuma nuna cewa abokan cinikin wutar lantarki na cikin gida da na waje sun biya basukan da suka gabata. An lura cewa abokan cinikin ƙasashen waje guda biyu sun biya kusan dala miliyan 5.19, yayin da abokan hulɗa guda takwas a Nijeriya suka biya kusan miliyan N505.71.

By ukarofi