Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da kashin farko na aikin babban titin Sakwato zuwa Badagry, wanda ke da nufin inganta hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a yayin addamar da wani taro na kwanaki biyu na ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta tarayya da hukumominta a Abuja ranar Talata.
Babban titin Sokoto-Badagry zai ratsa kusan jihohi tara, wanda zai inganta hanyoyin sufuri a wannan hanyar.
Baya ga aikin babbar hanyar, Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da gina madatsun ruwa guda 63.
Ana sa ran waɗannan madatsun ruwa za su ƙara ƙarfin samar da wutar lantarki a aasar da kuma tallafawa ci gaban aikin gona.
Alhaji Idris ya jaddada muhimmancin rawar da ma’aikatar ta taka wajen isar da sahihancin ƙoƙarin gwamnati na isar da ribar dimokuraɗiyya ga al’ummar Nijeriya.
Ya kuma bayyana buƙatar da ke akwai na ɓangarorin yaɗa labarai da sassan da ke cikin ma’aikatar su samu zurfin fahimtar tsare-tsaren gwamnati.
