Shekh Abdullahi Saleh Pakistan ne sabon shugaban NAHCON

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON).

Farfesa Pakistan babban Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya wanda ya yi karatunsa a Jami’ar Madinah da kuma Jami’ar Peshawar da ke Pakistan.

Shekh Pakistan ya ƙware a harkokin da suka shafi aikin Hajji, sannan ya taɓa rike shugabancin hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano.

Cikin sanarwar da Mashawarci na Musamman ga Shugaban kasa kan yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ƙasar ya buƙaci sabon shugaban hukumar yayi amfani da ƙwarewar da ya ke da ita don gudanar da aiki tuƙuru wajen sauƙe nauyin da aka ɗora masa.

Naɗin nasa zai tabbata ne bayan majalisar Dattawan Najeriya ta tantance shi.

By Babaji