Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula Tacewa da Haƙo Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce ba za ta amince da “babakere” a fannin mai da iskar gas ba.
Hakan ya biyo bayan ƙarar da Kamfanin Mai na Dangote ya shigar na neman yinnwatsi da lasisin shigo da man da NMDPRA ta ba wasu kamfanonin sayar da mai.
NMDPRA, a cikin takardar ƙarar da ta shigar a kan ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1324/2024, ta tabbatar da bayar da lasisin shigo da man fetur ga Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) Limited, AYM Shafa Limited, A. A. Rano Limited, T. Time Petroleum Limited, 2015 Petroleum Limited da Matriɗ Petroleum Serɓices Limited.
Da yake roƙon kotun da ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta da kuma gazawa, NMDPRA ta bayyana cewa matatar Dangote ba ta da haƙƙin samun ko ɗaya daga cikin abubuwan da ta ke nema.
Ta bayyana cewa matatar man dangote a halin yanzu har yanzu ba ta cika wadatar albarkatun man fetur na ƙasa ba.
NMDPRA ta ƙara da cewa, a bisa rashin wadatar matatar man Dangote da kuma bin sashe na 317 [9] na dokar PIA (Dokar Masana’antar Man Fetur), ta bayar da lasisi ga kamfanonin da ke da kyawawan bayanan kasuwancin da ake sayar da mai na ƙasa da ƙasa domin shigo da man fetur don cike giɓin da ake samu.
Da yake bayar da hujjar cewa an kuma ba ta damar inganta gasa da kuma hana cin zarafin manyan kasuwanni, NMDPRA ta ce alhakinta ya haɗa da hana cin hanci da rashawa a ɓangaren mai da iskar gas.
