Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta amince da ƙarin kashi 50 cikin 100 na harajin kiran waya a ranar Litinin, wanda zai iya ƙara yawan cajin kuɗin kiran waya zuwa N16.5 a minti ɗaya.
Dangane da bayanan harkokin tarho na ƙasa na 2023, wannan ƙarin kuɗin zai iya samar da sama da Naira Tiriliyan N6.74 a cikin kuɗaɗen shiga ga kamfanonin sadarwa a 2025 idan adadin kiran ya tsaya tsayin daka, don haka ‘yan Nijeriya na iya biyan wannan adadin ga kamfanoni.
Bugu da ƙari, wannan hasashe ya keɓanta tasirin tallan kira na kyauta da rangwame, wanda zai iya canja ainihin adadin kuɗaɗen shiga.
Wani bincike da hukumar NCC ta fitar na sabuwar shekarar 2023 na ‘Subscriber/Network Performance Report’ ya nuna cewa, a shekarar 2023, yawan harkokin amfani da wayar tarho ya kai mintuna biliyan 205.3, yayin da zirga-zirgar fita da shigar kira ta tsaya a kan mintuna biliyan 203.2.
Rahoton ya ƙara da cewa, “Ya zuwa watan Disamba na shekarar 2023 jimillar zirga-zirgar kiran waya na cikin gida na ƙasa sun kai mintuna 205,298,114,995.11 yayin da jimillar zirga-zirgar kiran waya a ƙananan hukumomi ta kai mintuna 203,187,588,876.00. MTN ne ke da mafi yawan harkokin kiran waya da masu amfani 122,667,600,437.00 da 123,762,501,615.00 a shekarar 2023.
Wannan yana nuna cewa ‘yan Nijeriya sun kashe kusan mintuna biliyan 408.5 suna kiran waya a gida a cikin 2023.
Tunda har yanzu babu sabbin bayanai na 2024, bincikenmu ya dogara ne akan bayanan da aka samu a 2023, wanda zai iya bambantawa a 2025.
