Matar Ekweremadu ta koma Nijeriya bayan sakinta daga kurkukun Birtaniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Maiɗakin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ike Ekweremadu, wato Madam Beatrice Ekweremadu, ta koma Nijeriya bayan sakinta daga kurkuku a Birtaniya.

Jaridar Vanguard ta Nijeriyar ta ruwaito cewa ta samu labarin komawarta ne daga wata majiya mai tushe.

A watan Maris na 2023 ne kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam.

Shari’ar ta shafi ɗauko wani ɗan Nijeriya mai shekara 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa ‘yar Ekweremadun.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekara 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa ƙoda.

Masu shigar da ƙara sun ce za a cire ƙodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ‘yar Ekweremadu mai shekara 25.

A lokacin kotun ta yanke wa tsohon shugaban majalisar dattawan ɗaurin shekara 10.

By ukarofi