Shugabannin ƙananan hukumomi sun yaba wa Gwamnan Kano kan raba wa ɗaliban firamare ‘uniform’ kyauta

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin Kano a jawabansu daban-daban sun yaba wa Gwamnan Kano kan raba kayan makaranta ga ɗaliban makarantun firamare a jihar.

Shugaban ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume, wanda ya ce ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi da ya jagoranci ayarin jami’an ƙaramar hukumar Kabo, wajen zuwa gidan gwamnatin Kano a lokacin bikin raba kayan makaranta na ‘yan firamare kimanin dubu 800 da Gwamna Kano Alhaji Abba kabir Yusuf ya yi a wannan lokaci.

Ya ce abun a yabawa Gwamnan Kano ne kuma abu ne da ya kamata gwamnonin jihohi Nijeriya da su yi koyi da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na kishi ilimi, da sauran fannoni wanda haka ce ta sa gwamnan Kano ya samu kyautar karramawa da yabawa akan ilimi.

Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo Alhaji Dr. Mani Tsoho, ya ce rabawa makarantu kayan makaranta a kano abu ne da bamu gani ba a shekara 8 da su ka wuce dan haka Abba ya cancanci a yi koyi da shi wajen ayyukan alkairi da ya gada daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan wannan alkairi, kuma wannan ce ta sa dole shugabannin ƙananan hukumomi su zage damtse wajen koyi da Gwamna Abba.

Shi kuwa Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Gezawa Aminu Abdulra’uf, ya ce ware kashi 30 da ware kashi 31 a kasafin kuɗin bara da bana kwalliya ta biya kuɗin sabulu kamar yadda muka gani a Gezawa hukumar CRC ta gyara mana makarantu huɗu da azuzuwa masu yawa kuma ana cigaba da aikin har yanzu a ko ina a Gezawa da ma sauran ƙananan hukumomi nasan haka abun ya ke, a ko ina a kano musamman wajan rabon littattafai da sauran kayan karatu da Gwamna Abba ya ke yi a ko yaushe.

A ƙarshe su ma sakatarorin ilimi na ƙaramar hukumar Kibiya Baba Ladan, da Sakataran ilimi na ƙaramar hukumar ƙaraye Mainasara Muhammad ƙaraye, Hajiya Maryam Aliyu Fanda sakatariyar ilimi ta ƙaramar hukumar Albasu, Idris Ibrahim Indabo sakataran ilimi na ƙaramar hukumar Wudil, da sauran sakatarori da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran su, sun ya bayawa Abba kan rabawa yara kayan makaranta kyauta a Kano.

By ukarofi