Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

Inter Milan da Borussia Dortmund na ƙyalla ido kan ɗan wasan tsakiya na Ingila, Jack Grealish mai shekara 29, ganin cewa babu tabbas game da ci gaba da zaman shi a Manchester City.

AC Milan na tunanin ɗaukar aron ɗan wasan gaba na Manchester United, Rasmus Hojland mai shekara 21 a duniya da kuma Joshua Zirkzee mai shekara 23.

Juventus ta tattauna da Udinese kan sayen ɗan wasa Thomas Krintensen mai shekara 23, wanda Tottenham da Leicester City ke ƙyalla ido a kansa.

Napoli na fatan za ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 50 domin ɗauko ɗan wasan gefe na Manchester United da kuma Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20.

Aston Villa ta yi watsi da tayin da West Ham ta yi mata na fam miliyan 57 kan ɗan wasan gaba Jhon Duram, kasancewar Villa ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan gaban na Columbia mai shekara 21 wanda darajarsa ta kai fam miliyan 80.

Manchester United na tattaunawa domin ɗaukar ɗan wasan baya Patrick Dorgu daga Lecce, inda ake sa ran ɗan wasan mai shekara 20 zai iya cike givin da ake da shi a ƙungiyar da Ruben Amorim ke jagoranta.

Mai horas da ƙungiyar Real Madrid, Carlo Ancelotti na tattara kayansa domin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, kuma ana ganin cewa kocin Bayer Leverkusen, ɗabi Alonso ne wanda ya fi cancanta ya maye gurbin Ancelotti, ɗan asalin ƙasar Italiya.

ɗan wasan Manchester United da Brazil, Antony, mai shekara 24 na daf da kammala yarjejeniyar komawa Real Betis a matsayin aro.

Juventus da Borussia Dortmund na matsa ƙaimi domin ɗaukar ɗan wasan baya na Chelsea da Portugal, Renato Veiga, wanda a yanzu zai iya tafiya a matsayin aro ko kuma tafiyar dindindin.

Marseile ta zama ƙungiya ta baya-bayan nan da ta nuna sha’awar ɗaukar Marcus Rashford daga Manchester United.

Sai dai Rashford ya fi son tafiya Barcelona, ƙungiyar da a yanzu ta tanadi kuɗin da za ta iya ɗaukar matashin ɗan asalin Ingila.

Manchester City ta ta cimma yarjejeniyar baka da Real Valladolid mai buga gasar La Liga domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya ɗan asalin Sierra Leone, Juma Bah, mai shekaru 18.

Tsohon ɗan wasan Manchester United ɗan asalin Faransa, Paul Pogba ya ce ya ƙi amincewa da tayin wata ƙungiya da ta so ta ɗauke shi a Rasha.

Derby County ta shafa wa fuskarta toka ta yi fatali da tayin da Brighton ta yi mata na ɗaukar ɗan wasanta na tsakiya Eiran Cashin, mai shekara 23 a duniya.

Nottingham Forest ta mayar da hankali sosai kan neman ɗan wasan gaba na Wolves da Brazil, Matheus Cunha a wannan wata na Janairu a ƙoƙarinta na riƙe wuta domin ganin ta je gasar zakarun Turai ta Champions League.

Arsenal ma ta nuna aniyarta ta sayo Cunha mai shekara 25 a wannan Janairu.

Chelsea na shirin ci gaba da tattaunawa da Manchester United domin ɗaukar ɗan wasan Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 20, wanda aka yi wa kuɗi fam miliyan 50.

Chelsea na son a zube mata tsabar kuɗi aƙalla Yuro miliyan 70 kafin ta bar ɗan wasanta na gaba ɗan asalin Fransa, Christopher Nkunku ya tafi Bayern Munich.

By ukarofi