Real Valladolid ta zargi Man City da zuga Bah ya soke kwantiraginsa

Spread the love

Real Valladolid ta zargi Manchester City da ƙarfafa gwiwa ga ɗaya daga ’yan wasanta, domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga gasar firimiyar Ingila.

Mai tsaron baya, Juma Bah ya sanar da ƙungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma Manchester City kan kankanin kuɗi.

Tun a baya City ta nemi izinin Valladolid, domin tattaunawa kan sayen matashin mai shekara 18, domin ya koma taka leda a Etihad.

Bah bai halarci atisaye ba ranar Laraba, inda hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta tabbatar cewar ya biya sauran ƙunshin kwantiraginsa a ƙungiyar, domin ya kara gaba.

Valladolid ta ce matakin da matashin ya ɗauka City ce da wakilin ɗan wasan suka kitsa komai, ta kuma yi wadai da wannan lamarin.

Mai shekara 18 ya koma Valladolid daga AIK Freetong, domin buga wasannin aro a bara, inda a watan nan Valladolid ta mallaki ɗan wasan.

Sai dai Bah yana kan tsarin yarjejeniya ta matashin ɗan wasa, amma bai amince ya saka hannu ba kan kwantiragi a matakin ƙwararren ɗan wasa ba.

Valladolid ta ce za ta ɗauki mataki na shari’a kan Bah, za kuma ta yi dukkan abinda ya kamata domin ta kare martabarta.

By ukarofi