Lawal Daura ya yi alƙawarin samar da tsaro da inganta rayuwar al’ummar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Malam Lawal Musa Daura, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a shekarar 2027, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da tsaro da bunƙasa rayuwar al’ummar jihar.

Lawal Musa Daura wanda tsohon darakta janaral na hukumar DSS ta ƙasa ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar yayin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Daura ya ce matakin da ya ɗauka na shiga takara ya biyo bayan tuntuɓa da ya yi da masu ruwa da tsaki da kuma kiraye-kirayen da ya ce ya samu daga al’ummar jihar masu neman sauyi a harkokin shugabanci.

Ɗan takarar ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a Katsina, yana mai cewa lamarin ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da kawo cikas ga harkokin noma da tattalin arziki a yankuna da dama na jihar.

Tsohon jami’in tsaron ya ce duk da kuɗaɗen da aka shafe shekaru ana kashewa a ɓangaren noma da tsaro, har yanzu manoma da dama ba sa iya komawa gonakinsu, yayin da wasu ke fama da rashin kayan aikin noma, iri masu inganci da hanyoyin ban ruwa.

Lawal Musa Daura ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bunƙasa noma, samar da ayyukan yi ga matasa, inganta kiwon lafiya da ilimi, tare da tabbatar da shugabanci mai gaskiya da riƙon amana.

A cewarsa, daga cikin shirye-shiryensa akwai gyaran manyan madatsun ruwa irin su Ajiwa, Safke, Mairuwa da Zobe domin bunƙasa noman rani da samar da ruwa ga manoma.

Haka kuma ya yi alƙawarin samar da ingantattun kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata a asibitocin gwamnati tare da inganta makarantun gwamnati ta hanyar ɗaukar malamai da samar da kayan koyarwa.

Dan takarar ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan kare muhalli da dakile matsalolin kwararowar hamada, sare bishiyoyi da sauyin yanayi.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su mara masa baya domin samar da Katsina mai tsaro, haɗin kai da ci gaban tattalin arziki.

By ukarofi