
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa (NRC) ta ce layin dogo na Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki nan da mako mai zuwa.
Hakan ya biyo bayan kammala gyara a sashen da ya lalace da kuma nazari a kai daga ƙwararru game da inganci tsaronsa, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a, Callistus Unyimadu ya bayyana.
Ya ce, za a sanar da ƙarin bayani akan al’amarin da kuma ranar da za koma aikin nan ba da jimawa ba.
Jami’in ya bayyana cewa, tun da aka ɗauki matakin dakatarwar na wucin-gadi bayan gocewar wani jirgi da ya nufi Kaduna daga Abuja, hukumar ta ke aiki tuƙuru wajen tabbatar da warware matsalar bisa inganci da nagarta kamar yadda ake yi a tsarin layukan a ko’ina a duniya.
NRC ta kuma ce, a ƙoƙarinsa na kula da walwalar fasinjoji, ta mayar wa mutane 512 kuɗaɗensu daga cikin fasinjoji 583 da ke cikin jirgin a lokacin da abin ya faru.
Ta ƙara da cewa, ana ƙoƙarin ganin su ma sauran fasinjojin da suka rage a mayar musu da kuɗaɗen nasu.
