Layin lantarki na Benin-Omotosho katsewa ya yi, ba lalacewa ba – TCN

Daga BELLO A. BABAJI

Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN, ya ce rumbun lantarki na ƙasa bai lalace ba, kamar yadda kafafen labarai ke yaɗa wa al’umma.

A ranar Asabar 11 ga watan Junairu da misalin ƙarfe 1:41 na rana ne layin Osogbo-Ihovour ya tsinke wanda ya faru ne sakamakon katsewa da na Benin-Omotosho ya yi inda ya shafi raba adadi mai yawa na wuta ga yankin Legas.

Wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah ya fitar, ta ce gabannin katsewar, megawat 4,335.63 ne adadin nauyin wutar da rumbun ya raba, yayin da ya koma megawat 2,573.23 bayan aukuwar lamarin wanda ke nuna cewa babu batun lalacewa game da shi.

Layin da ya katse ya shafi yankunan Egbin, Olorunsogo, Omotosho, Geregu da Paras waɗanda a halin yanzu an gyara su, sai kaɗai na Benin-Omotosho wanda ake ƙoƙarin kammala aikin gyaransa.

Jami’in ya kuma ce yayin da TCN take ƙoƙarin shawo kan matsalar, ya na da muhimmanci a fahimci illar yaɗa labaran da suke ƙunshe da kurakurai ga al’umma da gangan da kuma amfanin bayyana abubuwan da suke na gaskiya.