Lokaci ya yi da Turai za ta fice daga tarkon Amurka!

Daga CMG HAUSA

A jiya Laraba bisa agogon Amurka, majalissar wakilan ƙasar ta kaɗa ƙuri’u, na hana shigar da ɗanyen mai da iskar gas da kwal na ƙasar Rasha cikin Amurka. Ya zuwa yanzu, wannan shi ne mataki mafi tsauri da Amurka ta ɗauka cikin jerin takunkumai kan Rasha. To sai dai kuma, al’ummun nahiyar Turai na kallon matakin a matsayin takunkumi kan Turai maimakon Rasha!

Ko shakka babu, ra’ayin na su na kan turba. Tun bayan ɓarkewar rikicin Rasha da Ukraine, ba tare da la’akari da tarihin matsalolin Ukraine ba, da irin tasirin da ƙara matsawar NATO zuwa gabashi zai haifar, Amurka ta yi haɗin gwiwa da ƙawayenta na Turai, wajen ƙaƙaba wa Rasha takunkumai. Sai dai kuma rashin lura da illar takunkuman, ya sa ƙasashen Turai tsintar kan su cikin mummunan tasirin tashin hankalin dake gudana.

Fassarawa: Saminu daga CMG Hausa