Ministocin Wajen Sin da Italiya sun zanta game da halin da ake ciki a Ukraine

Daga CMG HAUSA

Babban ɗan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya zanta ta kafar bidiyo da takwaransa na Italiya Luigi Di Maio a yau Alhamis, inda suka yi musayar yawu game da halin da ake ciki a ƙasar Ukraine.

Wang Yi ya jaddada cewa, batun tsaron Turai na cikin muhimman al’amura, masu nasaba da rikicin Ukraine. Ya ce kamata ya yi ƙasashen Turai su zurfafa shawarwari tsakanin su da Rasha, bisa yarjeniyoyin da aka cimma kawo yanzu, ta yadda hakan zai ba da damar fitar da tsarin tsaron Turai mai nagarta, da tasiri kuma mai dorewa, kana a kai ga cimma daidaito na tsawon lokaci a nahiyar.

Fassarawa: Saminu daga CMG Hausa