Ma’aikacin Leadership Hausa, Sabo Ahmad ya rasu

Jaridar Leadership Hausa ta rasa shugaban sashen fassara, Malam Sabo Ahmed Kafin-Maiyaki wanda ya rasu a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2023 yana da shekaru 54 a duniya bayan doguwar jinya.

A cewar Leadership Hausa, sanarwar da iyalansa suka fitar, Malam Sabo ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10 da kuma ɗan uwa guda ɗaya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a yi jana’izarsa a ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu, 2023 a Samaru, Zariya, a Jihar Kaduna.

Da yake ƙarin haske, Editan Leadership Hausa, Abdulrazaq Yahuza Jere, ya bayyana Malam Sabo a matsayin babban ginshiƙin sashen Hausa.

Sabo kuma shi ne mai kula da shafin laifin kotu da dan sanda na Leadership Hausa.

Jere ya kuma jajanta wa iyalan mamacin, inda ya bayyana alhininsa game da rasuwar ma’aikacin da suka yi aiki tukuru cikin aminci.

Ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga ɗaukacin sashen na Hausa da kuma kamfanin jaridar Leadership baki ɗaya.

Ya roƙi Allah Maxaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma sada shi da Aljanatul Firdausi.

“Allah ya bai wa iyalansa juriyar wannan rashi da suka yi.”